Labarai duniya labarai Hausa kannywood BBC news

Hadarin jirgin sama na alhazai a Kano..

A Rana Mai Kamar Ta Yau 23 Ga Watan Junairu 1973 Wani jirgi kirar Boeing 707 da aka yi hayarsa ya kama da wuta lokacin da ya sauka a filin jirgin saman Kano, Najeriya , inda ya kashe mutane 176.

Hadarin jirgin saman na Kano ya kasance jirgin fasinja Boeing (707) da aka yi haya a ranar (22) ga watan Janairun shekara ta alib (1973) wanda ya yi hadari yayin da yake kokarin sauka a Filin jirgin saman Kano. Wannan shi ne hadari mafi hadari na jirgin sama da ya taba faruwa a Najeriya, yayin da fasinjoji (176) da ma’aikata suka halaka a cikin hadarin. Akwai (22) da suka tsira.

A 1973, wani jirgin sama dauke da Alhazan da suka kammala aikin Ibadar Hajji da kasa mai sarki ya samu hadari yayin da yake kokarin sauka a babban filin jirgin saman Malam Aminu Kano in da akayi zaton mutane 1706 sun rigamu gidan gaskiya. Mutane 22 ne su ka tsallake rijiya da baya; wannan ya hada da matukin jirgin da ma’aikatan jirgin, bisa ga rahoton New York Times.

Wannan shine hadarin jirgi mafi tayar da hankali zuwa lokacin. Gabanin 1973, jirgin kasar Rasha ne ya taba hadari inda mutane 176 suka hallaka. Jirgin mahajjatan mai kirar Boeing 707, mallakan kasar Jordan na daya daga cikin jiragen da ke jigilar mahajjatan Najeriya zuwa kasar Saudiyya a lokacin.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin ya kama da wuta ne yayinda ya nufi filin jirgin saman Kano. Amma dai ba’a tabbata ko jirgin ya taba kasa ba a lokacin.

mun gode sosai da sosai masoya bisa musamman gidan labari masu inganci na dpvmict. Come..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button